Wakilcin Kura, Madobi Da Garun Malam Ba Ta Sake Zani Ba

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga USMAN SULEIMAN SARKI

Tun dawowa mulkin dimokaradiyya a shekara ta 1999, Kananan hukumomin Kura, Madobi da Garun Malam sun samu wakilai guda hudu da suka yi wakilcinsu a majalisar tarayya amma har ya zuwa yanzu ba ta sake zani ba, domin wakilan ba su iya tabuka komai na a zo a gani ba, duk da suna samun kaso na aiwatar da ayyuka da aka fi sani da ‘Constituency Project’.

Babban abin takaici shi ne yadda aka samar da Wakilin wadannan kananan hukumomi mai ci a yanzu wanda al’ummar wadannan yankuna suka gamsu da cewa ba wai bukatunsu ne a gabansa ba duba da rashin tabuka wani abin a zo a gani cikin shekara guda da ya yi yana wakilcin.

Abin tambaya a nan shi ne, shin wakilin ya zagaya neman kuri’un al’umma? Idan ya je wane allawari ya yi na kawo ayyukan ci gaban yankunan? Kuma a cikin me ya aiwatar ya zuwa yanzu? In kuma bai je yakin neman zabe ba, to anya dama ya san yankunan kananan hukumomin kuwa? Ko kawai takara ya samu a sama? Idan bai san yankunan ba to ya taba zagayawa a matsayinsa na wakili ya binciko matsalolinsu don taimakawa wajen warware su?
Na tabbatar akwai wakilai sababbi irinsa wanda shigarsu majalisa karon farko kenan wadanda ina da kudure-kudure da suka gabatar kuma ina da bayanai na ayyukan raya kasa da suka aiwatar na ‘constituency projects’ a yankunansu amma abin takaici shi wannan wakili namu ya gaza kawo wani aiki na raya kasa kuma babban abin bacin rai shi ne yadda ya wofintar da talakawa da suka zabe shi tare da rashin girmama shuwagabannin al’umma da sauran yan siyasa na wadannan yakuna wadanda sune suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin ya kai ga nasara.

A karshe ina mai kira ga yan uwana al’ummar wadannan yankuna na Kura, Madobi da Garun Malam musamman ‘delegates’ da mu farga kuma mu farka daga gyangyadi mu tsaya mu duba da idon basira domin tabbatar da samar da wakili nagari a shekarar zabe ta 2023 domin ta tabbata wannan wakili ba al’umma bace a gabansa domin ba shi da wata manufa ta kyautata rayuwar al’ummar da suka zabe shi.

Usman Suleiman Sarki
08058330007

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply