Wata Kungiya Ta Bukaci A Hada Hannun Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Nijeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Cibiyar kare hakkin bil adam ta ‘Centre for Human and Socio-economic Rights (CHSR)’ ta bukaci a hada hannun tare da jaddada bukatar a samar da karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Mr Alex Omotehinse, ya yi wannan kiran a tattauanwarsa da manema labarai a garin Legas ranar Litinin.

Ya ce, akwai bukatar hada hannu daga masu ruwa da tsaki don a kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.

Omotehinse ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su cire kabilanci tare da hada hannun don a kawo karshen ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a kasar nan.

“Mataki na farko na kawo karshen matsalar tsaro shi ne cikkaken hadin kai daga dukkan ‘yan Nijeriya.

“Dole mu kawar da kabilanci da banbancin addini a wajen kawo karshen wannan matsalar.

Share.

About Author

Leave A Reply