Wata Kungiya Ta Kaddamar Da Shirin Horas Da ‘Yan Mata 125 Sana’o’in Dogaro Da Kai A Zariya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wata kungiya mai suna ‘Arewa Girls Forum’ tare da hadin gwiwar ‘African Center for Education Development (CLEDA Africa)’ sun kaddamar da wani shiri na musamman don horas da ‘yan mata 125 sana’o’in dogaro da kai don tsayuwa da kakafunsu a harkokin yau da kullum na rayuwa.

Shugaban kungiyar CLEDA Africa, Mr Daniels Akpan, ya sanar da haka a tattauwarsa da manema labarai a garin Kaduna ranar Lahadi.

Akpan ya kuma kara bayyana cewa, shirin ya samu tallafin kungiyar ‘World Connect’ daga kasar Amurka tare da kuma hadin gwiwar ‘Youth Hub Africa’ da kuma gwmanatin jihar Kaduna.

Ya kuma ce, an kaddamar da shirin ne a garin Zariya za kuma a yi wata 2 ana horas da matan, ya ce , an zabo matan da za su amfana ne daga yankin Muchia a karamar hukumar Sabon Gari na jihar Kaduna.

Share.

About Author

Leave A Reply