Wata Kungiya Ta Nemi Gwamnonin Nijeriya Su Yi Koyi Da Gwamna Zulum Wajen Sadaukarwa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wata kungiya mai suna ‘Civil Liberties Organisation (CLO)’ ta bukaci gwamnonin Nijeriya su yi koyi da Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum akan yadda yake gudanar da ayyukansa cikin adalci da kuma yadda yake sadaukarwa ga al’ummarsa.

Shugaban kungiyar a jihar Amabara, Mr Vincent Ezekwueme, ya yi wanna kiran a yayin daya ke tattauna wa da manema labarai a garin Inugu ranar Litinin.

Shugagan kungiyar ya kuma ce, sun yaba da yadda Zulum ya saka wa wani Likita mai suna Dr Isah Akinbode dan asalin jihar Ogun wanda ya sadaukar da rayuwarsa duk da rikicin Boko Haram yana cigaba da ba al’umma magani a asibitin garin Mongono.

“Saboda kishin kasa na Gwamnan ya tallafa wa likita Dr Akinbode da kudi Naira miliyan 13.9 da motar hawa, wanda ya yi aiki ba kakkautawa a jihar Borno na tsawon shekara 22.

Ezekwueme ya kuma yaba wa Zulum akan yadda ya karawa wata Malaman makaranta mai suna Mrs Obiageli Mazi, girma akan yadda take aikin koyar da yara duk kuwa da rikicin da ake ciki, akan haka ya bukaci gwamnonin su yi koyi da irin  wannna hali na Gwamna Zulum.

 

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply