Wata Mahanga Daga Jawabin Buhari Na Sabuwar Shekara, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jigo a tsarin shugabanci na Dimokradiyya shi ne jagoranci na gari da yin komi a bayyane. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da wannan a jawabin da ya yi wa ‘yan kasa na murnar zagayowar sabuwar shekarar 2021.

Wannan jawabin ya samarwa da Shugaba Buhari damar yin bayani kaitsaye ga al’ummar da suka zabe shi. Shugaba Buhari ya yi bayani kan irin nasarorin da gwamnatins ta samu a shekarar da ta gabata ta 2020 da kuma abubuwan da za a yi tsammani daga gwamnatinsa a sabuwar shekara.

Wannan jawabin ya fayyace cancanta, kwarewa da cikakkiyar lafiyar Shugaban Kasa Buhari. Gwamnatin Buhari ba ta yin kasa a gwiwa wurin ganin ta cimma manufofinta a bangaren tsaro, tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa. Dukkan wadannan bangarorin sai da Shugaban Kasa Buhari ya warware su a sakonsa ga ‘yan Nijeriya.

Haka nan kuma jawabin ya nuna dalilin da ya sa Gamayyar Kungiyar Kasashen Afirka suka zabi Buhari da ya jagoranci gangamin yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar. Wannan kuwa sun zabe shi ne don irin jajircewarsa kan yaki da rashawa.

A idon kowa, karkashin mulkin shugaban Kasa Muhammadu Buhari an daure mashahuren ‘yan siyasa. Wanda hakan ta yiwu ne saboda ikon da ya ba Hukumar Yaki da Rashawa, wacce a baya ta rasa wannan karfin. Cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da aka kama akwai tsoffin gwamnonin Taraba da Filato, wato Joshua Dariye da Jolly Nyame. Wanda duk cikarsu suna gidan yari.

Ba don kotu ta sallame su a ‘yan kwanakin baya ba, tsohon gwamnan Abiya, Orji Uzor Kalu da tsohon kakakin PDP, Olisa Metuh duk sai da EFCC ta daure su.

A jawabinsa na sabuwar shekara, Shugaba Buhari ya jaddada yunkurin gwamnati na samar da sabbin tsare-tsare da dokokin da za su karawa hukumar yaki da rashawa karfi, ta yadda za ta yi aikinta cikin natsuwa har ta kai ga samun nasara.

Kamar yadda Shugaba Buhari ya bayyana, shirin gwamnatinsa na inganta bangarorin jami’an tsaro, kama daga soja zuwa ‘yan sanda don magance matsalolin tsaron da ke fuskantar Nijeriya, zai kawo karshen duk wata kayar baya da ta’addanci da ake fama da su a wasu sassan kasar. Wannan batu, ya yi matukar farantawa ‘yan Nijeriya rai.

A cikin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya kawo batun sace daliban Sakandare sama da 300 a garin Kankara ta Jihar Katsina. Yanayin gaggawar ceto yaran da jami’an tsaro suka yi, ita ma wata ‘yar manuniya ce ga irin kokarin da gwamnatin Buhari ke yi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci Babban Bankin Nijeriya wato CBN da kada bankin ya bayar da tallafi ga masu shigo da kayan abinci. Wannan wani umurni ne kebantacce da Shugaban ya ba babban bankin akan hana tallafi ga masu shigo da abinci daga wasu kasashen. Abin da gwamnatin ta Buhari ke son yi shi ne ta sa manoman Nijeriya su samar da abincin da za mu iya dogaro da kanmu. Wanda wannan shi ne silar ci gaba da samun daukaka ga duk wata kasa a duniya.

Daga shekarar 2015 zuwa yau, bayan zuwan wannan gwamnati ta Shugaba Buhari, an ga irin nasarorin da ya kawo a bangaren raya kasa, wanda ko makaho ya san an yi wani abu. Kuma wannan ayyukan da aka yi ko zuwa nan gaba za a ci moriyarsu.

A dalilin ganin an yi ayyukan raya kasa da za su amfani jama’a ne ma ya sa Shugaban Kasa Buhari ya nada tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Fashola a matsayin ministan ayyuka. A karkashin kulawar Fashola ne gwamnatin Buhari ta fara gina Gadar Neja ta biyu bayan da ta farkon ta lalace, wacce aka gina ta tun zamanin Firaminista Tafawa Balewa a shekarar 1965.

A gabadaya fadin Kasar muna shaidar yadda ake ta yin ayyukan raya kasa. Daga sabbin gine-gine, gina taragon jiragen kasa, ginin manyan hanyoyi da gadoji, wannan kuwa a birane da kauyuka na fadin Nijeriya.

Fiye da kowanne lokaci, an samu ci gaba sosai a harkar kasuwanci a Nijeriya. An samu nasarori masu dama a bangaren wutar lantarki. Ba tare da tantama ba, saboda irin aikin da aka yi a bangaren wutar lantarkin, tabbas za a wadata da lantarki wanda zai taimakawa masana’antu da bunkasar kasuwanci.

A matsayin gwamnatin da ke da muradin cimma manufa, Gwamnatin Buhari ta ci gaba da kasancewa kan turba. A lokacin da ya zama wajibi sai an kulle boda, Buhari bai yi kasa-a-gwiwa ba, ya kulle. A yanzu kuma da dama ta bayar na za a iya budewa, sai ya sake bayar da umurnin a bude iyakokin.

Sai kuma me? A jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da makwaftanmu da ke Afirka ta Yamma cewa Nijeriya ta bude iyakokinta ga wadanda ke son yin halastattun kasuwanci.

Ya sanyaya zukatan jama’a da zantukansa a kan irin wahalhalun da ‘yan kasa ke sha yayin da ake tsaka da yin gyara. A matsayinsa na Uban kowa, ya yi alkawarin cewa komi zai daidaita . Ya kuma karyata tare da kunyata masu burin ganin kasar ta tsaya cik! Inda ya ce, Nijeriya ci gaba ta yi ba baya ba.

Daga cikin halinsa na tausayi, a jawabin sabuwar shekarar, Shugaba Buhari ya nuna damuwa da zanga-zangar matasa, har ma ya ce, gwamnatinsa za ta yi wa tsarin Rundunar ‘yan sanda garanbawul.

Daga karshe, Shugaban Kasa Buhari ya tabbatar wa da ‘yan Nijera cewa a matsayinsa Kwamandan Askarawa, zai yi duk wani abu da ya dace wurin fuskantar matsalolin da ke addabar Nijeriya har sai an warware su.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Share.

About Author

Leave A Reply