Wata Sabuwa: Ramos Na Son Komawa Manchester United

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A wani sabon rahoto, Kungiyar Manchester United na son sayen dan kwallon baya Sergio Ramos.

Ana ci gaba da zaman dar-dar ne a Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yayin da kwantiragin Ramos ke gab da karewa. Sakamakon haka ne a ke ta kyautata zaton Kungiyar PSG ta kasar Faransa ta matsa wurin neman dan wasan.

Sai dai daga zantuka da ‘yar manuniyar da Ramos ya nuna, ya ce, ya fi muradin ci gaba da buga wasa a Firimiyar Ingila.

Idan dai ba a manta ba tun a shekarar 2015 Manchester United ta yi yunkurin sayen dan kwallo Ramos, inda hakar tasu ta ki cimma ruwa.

 

Share.

About Author

Leave A Reply