Wata Sabuwa: Rikici Ya Barke A Zaben Shugabannin PDP Na Jihar Neja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

An dage zaben shugabannin jam’iyyar PDP na Neja, sakamakon rikicin da ya barke.

 

‘Yan bangan siyasa masu alaka da mutum  biyu da ke takarar Shugabancin jam’iyyar sun yi fito-na-fito ne a wajen, lamarin da ya sa aka kashe zaben.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa rikicin ya barke ne bayan wasu jami’an tsaro sun bugi tsohon dan Majalisar wakilai, Alhaji Baba Agaie, inda daga baya suka yi awun gaba da shi.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun misalin karfe 7:00 na safe, magoya bayan ‘yan takarar suka mamayi Sakatariyar jam’iyyar ta PDP da ke Western Bypass a Minna duk da jami’an tsaron da ake jibge a harabar wajen.

 

Wasu rahotannin na nuni da cewa wasu ‘yan jam’iyyar ne daga karamar hukumar Agaie suka tara wa Alhaji Baba Agaie gajiya.

 

Magoya bayan sun zargi Agaie da yi musu zagon kasa ta hanyar kulla alaka da tsohon gwamnan jihar, kuma uba a jam’iyyar Dakta Babangida Aliyu.

 

Sai dai, da rikicin ya yi kamari, sai jami’an tsaro suka fitar da mambobin Kwamitin zaben karkashin jagorancin Malam Mohammed Imam daga Sakatariyar.

 

Fitattun ‘yan takarar a zaben mutum biyu ne; Tanko Benji, Shugaban jam’iyyar mai ci wanda yake neman tazarce, sai kuma Alhaji Mukhtar Ahmed.

 

Share.

About Author

Leave A Reply