Yadda Kasurgumin Barawo Ya Yi Layar Zana A Ofishin ‘Yan Sanda A Bauchi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +
Daga Nasiru Hassan
Abu kamar wasa sai ga shi ya zama gaske,inda a yammacin  Ranar Talata 12 ga watan Mayu wani babban barawo da ke tsare a hannun jami’an ‘yan sanda na Yalwa Division da ke cikin garin Bauchi yayi batan dabo, lamarin da ya tada hankulan jami’an ‘yansanda da ke wannan caji ofis kana abinda ya kai ga garkame wani dansanda mai mukamin sufeto.
Al’amarin da ke zama tamkar wani dirama dai ya faro ne a ranar Litinin 11 ga wannan wata na Mayu, ranar da wani bawan Allah mai suna Muhammad Sanusi daga kauyen Miya ta karamar hukumar Ganjuwa ya shigo cikin garin Bauchi da nufin sayen manja domin sayarwa. Sai dai bayan ya sauka a mota a kusa da shataletalen Awalah, ya shiga kekenapep da nufin isa kasuwar Muda Lawal sai ga wani fasinja shi ma ya shiga kekenapep din. Bayan sun gaisa da Muhammad Sanusi, cikin sakin fuska ya tambaye shi daga ina yake? Sai ya amsa masa da cewa daga garin Miya yake. Budan bakin wannan mutumin sai ya ce masa ba ka san an hana mutanen kauye shigowa ba ne? Nan take mutumin ya ciro katin shaidar dansanda ya nuna masa, kana yace ya kama shi a bisa laifin shigowa cikin gari. Daga nan kuma ya zaro ankwa ya daure hannuwan Muhammad Sanusi da shi, sannan ya caje aljihunsa kana ya karbe kudade har Naira dubu dari shida wadanda ya zo da nufin siyan manja, sannan ya ce zai kai shi caji ofis.
Malam Abubakar Adamu wanda aboki ne ga yayan Muhammad Sanusi kuma ya shiga lamarin domin ganin an kwato wa kanin abokinsa hakkokinsa ya ci gaba da bayyana wa wakilinmu cewa bayan Muhammad Sanusi ya lura cewa tafiya ta ki karewa ba tare da an tsaya a caji ofis ba, sai yace shi bai bai yarda ba, ai an wuce ofisoshin ‘yansanda. Daga nan sai mai kekenapep din ya tsaya a unguwar Gwallameji kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi,  ya ce kekensa ta lalace. A wannan wuri ne mutumin ya fito da Muhammad Sanusi kana ya umurce shi da yayi ta yin tsallen kwado. Bayan ya fara, sai hankulan jama’a ya kai gare su, inda suka fara tambayar meke faruwa? A wannan lokaci ne Muhammad Sanusi ya Ankara cewa barawon ya hau ‘Kekenapep’, shi kuma ya tsala ihu yana cewa “Kudina fa?’’ A wannan hali ne mutane suka bi shi, shi kuwa barawon sai ya sauka, inda ya nufi wani lungu da ke kusa da hotal din Benco da ke Rafin Zurfi. Sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba domin da tallafin  jama’an gari an yi sa’ar kama shi.
Sai dai wani abin takaici da ya faru bayan damke wannan bata gari shi ne yanda mutane suka yi warwason kudaden da barawon ya karbe a hannun Muhammad Sanusi kuma ya zuwa lokacin hada wannan labari ba a kai ga gano ko mutum guda daga cikin su ba, kana tare da taimakon Sarkin Yamman Gwallameji an titsiya keyar barawon zuwa ofishin shiyya na ‘yansanda da ke Yalwa.
Bayan isar su caji ofis din Yalwan ne sai barawon ya kira wani dansanda mai mukamin sufeto a matsayin dan uwansa, kuma ko da ya iso ya tabbatar da cewa shi dan uwan barawon ne, kana ya tabbatar wa jami’an tsaron cewa barawon korarren dansanda ne, inda ya bukaci ganawa da shi. A yayin da suke ganawar ne sai wani bawan Allah mai suna Yusuf Munkaila Maianguwa ya tunatar da ‘yansanda illar hada cunkoso a wuri guda, wanda hakan ya sa ‘yansandan suka bukaci mutane da ke wurin da su ragu. Sai dai kash, a daidai lokacin da ake ficewa da cikin ofis din ne shi kuma barawon ya sulale, inda aka neme shi aka rasa.
Malam Abubakar Adamu yace ko da ya ji ‘yansandan na cewa barawon ya bace ba a gan shi ba, sai ya kada baki ya ce “wannan shi ake kira zancen banza.” Kana ya yi zargin cewa ‘yansandan sun saki barawon ne domin ya arce, zargin da nan take ya kada hantar jami’an
tsaron. Sai dai wani abin farinciki shi ne yanzu haka shi dansanda mai mukamin sufeton da ya zo a matsayin dan uwan barawon yana garkame a
hannun su.Wakilin Tantabara ya tafi wannan caji ofis da ke Yalwa domin jin ta bakin jami’an tsaron amma sun ce masa DPO ne kawai zai iya yin magana da shi a hukumance. To amma a gefe guda wasu jami’an ‘yan sandan da ba su yarda mu dauki sunayensu ko muryarsu ba sun tabbatar da faruwar wannan lamari. A gefe guda wakilin namu ya yi ta kiran Muhammad Sanusi domin jin ta bakinsa amma har ya zuwa lokacin aikawa da wannan rahoton bai dauki wayar ba, ya tura masa sakon kar ta kwana amma babu amsa.

Daga bisani ya kira DPO ta waya, inda cikin fushi yace
shi bai san wani abu mai kama da haka da ya faru a caji ofis dinsa.
Daga karshe wakilin namu ya kira jami’in hulda da manema labarai na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti, wanda ya shaida masa cewa a halin yanzu labarin bai iso gare su ba, amma zai bincika.
Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply