Yadda Makiya Da Mahassada Ke Kokarin Bata Sunan Dauda Lawal

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga SULAIMAN BALA IDRIS, Abuja

“Muna neman agajin abin da ba za mu iya yi wa kanmu ne daga jama’a”, Inji EMILE DURKHEIM

A lokacin da nake dalibi a Jami’a na shahara a matsayin masoyin Karl Marx, musamman yadda nake sanya tufafi, tumin sumar da ke kai na da kuma irin tsattsaurar matsayar da na ke da ita yayin tattaunawa a aji. Sunan Marx ya bi ni sosai ta yadda hatta wasu cikin malumanmu sun koma kirana da Marx. Yawancin lokutana a dakin karatu ‘Laburare’ na makaranta, ina cinye su ne wurin karanta litattafai a kan Karl Heinrich Marx fiye ma da darussan da aka koyar da mu a aji.

A duk tsawon wannan lokaci, daga lokacina a Jami’a zuwa yau, maganar gaskiya ita ce na fi tasirantuwa da Emile Durkheim fiye da Karl Marx din da ake danganta ni da shi. A karatuttuka kan Durkheim na fahimci mu’amalar zamani, bambanci a dabi’ar mutane, sauyin yanayi, binciken kimiyya fiye da duk wani masani a fannin kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar dan Adam. Tasirin da nazariyyar Durkheim ta yi min ta zarcewa ta Karl Marx.

A nazariyyar Durkheim ne na fahimci cewa, mutane ba su iya rayuwa sai da taimakekeniya a tsakaninsu. Duk bakin cikin mutum da hassadarsa, ba zai yiwu ya rayu ba sai da taimakon mutane. Kowanne mutum yana da kwarewarsa da fannin da ya fi wayo a cikinsa. Ba zai yiwu ka samu mutumin da ya ke kwararren likita ne ba, sannan kuma kwararren masanin kimiyyar dakile barna. Ba zai yiwu ka zama kwararre a fannin kama barayin gwamnati ba, sannan ka zama kwararre a fannin harkar banki da tattali. Kowa da kwarewarsa da kuma irin kiwon da ya amshe sa.

Wadannan misalai da na bayar a sama, sun isa hujjar fallasa irin mugun nufin da wasu marasa mutunci ke da shi, wadanda suke ta rura wutar kiyayye da gaba, wadanda ke ta yada maganganun karya da batanci a kan Dr. Dauda Lawal Dare. Duk da har cikin zuciyarsu sun san cewa, abubuwan da suke yadawa a kansa karya ne.

Dabi’a mai kyau ita ce muhimmiyar aba a rayuwar dan adam. Duk wanda bai da dabi’a mai kyau za ka ga rayuwarshi sai a hankali. Dakta Dauda Lawal Dare yana matukar taka-tsantsan wurin kiyaye dabi’arsa ta kirki, shi ya sa a duk inda ya tsinci kansa yake son yin komi bisa tsari, kiyaye doka da sanin ya kamata. Wai irin wannan mutumin ne wasu lalatattu suke ta hankoron sai sun bata mishi suna.

Dauda Lawal din da suke ta son batawa suna bai taba yin aikin gwamnati ba. A shekarar 2012 ne ya zama memba a bangaren gudanarwa ne shahararren Bankin First Bank, daga nan aka yi masa mukamin Babban Darakta mai kula sashen mu’amala jama’a, sannan kuma ya zama Babban Darakta mai kula da arewa. Kafin nan sai da ya taba rike mukamin mataimakin shugaba na sashen mu’amala da jama’a a yankin arewa, da dai sauran manyan mukamai a banckin, ciki har da jukamin ‘Business Development Manager’ a Maitama dake Abuja, inda ya yi amfani da kwarewarsa wurin daga darajar bankin zuwa mataki na gaba.

Yana da kwarewar sama da shekara 30 a sashen gudanarwa na harkar banki, wanda bayanai sun nuna cewa ya daga martabar bankin fiye da yadda yake a baya. Saboda irin aikin da ya yi na ciyar da bankin First Bank din gaba, Dauda Lawal ya samu lambar yabo da dama daga hukumar gudanarwar bankin.

Irin wannan mutumin da ya dade a harkar banki, ya ke da kwarewa da kiyayewa ne za a zarga da yin taimakawa wurin kawar da kudaden gwamnati? Ai kana ji ka san aikin mahassada ne wannan da makiya.

Ko ma mene ne manufar wadannan mutanen, sun yi a banza. Domin babu wanda zai yarda da wadannan karairayin nasu. Yadda lamurra suka nuna, mahassada da makiya sun fito kwansu da kwarkwata da zimmar batanci ga Dauda. Ba yau suka fara irin wannan ba, wai su damuwarsu Allah ya rufawa Dauda asiri, sannan Allah Ya ba Dauda zuciyar taimako da kaunar jama’a.

Idan kana son sanin wane ne Dauda Lawal, ka je Zamfara ka yi tambaya. Za ka ganewa idanuwanka alheri, za ka ga irin farin cikin da wannan bawan Allah ya sa a zukatan mutane. Ni shaida ne, ba wai jiyau ba ne. Na gani da ido na. Mutum ne mai son raya al’umma. Burinsa shi ne ya ga ana annushawa da farin ciki.

Su kuma masu son ganin bayansa, bakin cikinsu shi ne su ga ana farin ciki, ba su kaunar duk wani mai taimakon al’umma. Wannan ne babban dalilinsu, amma ai Allah ya fi su.

Daga karshe, su masu irin wannan aiki na hassada da makauniyar kiyayye, su sani cewa komi nisan jifa, kasa zai fado. Kuma ba a yi wa karya ado, gaskiya ce ke nasara kan karya. Lokaci zai nuna, kuma za a fayyace mai gaskiya. Lokacin jin kunyarsu ne yanzu, su ma kuma sun sani.

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply