‘Yan Kasuwan Nijeriya A Kasar Ghana Sun Nemi A Kawo Karshen Musguna Musu Da Ake Yi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

 

‘Yan Nijeriya da ke harkokin kasuwancin su a kasar Ghana sun bukaci gwamnatin taraya ta gagauta daukar matakan ganin an kawo karshen musgunawa da cin mutumcin da ake yi musu musamman daga hukumomin gwamnatin kasar Ghana.

Mr Chukwuemeka Nnaji, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar ‘Nigerian Union of Traders Association in Ghana (NUTAG)’ ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai ta wayar hannu ranar Litinin.

Yana magana ne bayan da hukumomin Ghana suka kama ‘yan Nijeriya fiye da 500 a garin Bolga, da ke yankin Upper West na kasar ta Ghana.

Ya ce, an kama mutum 500 aka kuma wuce dasu yankin Aflao ba tare da cikkaken binciken yadda suka shigo kasar ba, hukumar shige da fice na kasar ce ta yi wannan aikin.

“Wannan ba zai yiwu ba, muna matukar mutunta gwamnatin Ghana amma sau da yawa basa mutunta mu, akan haka muna bukatar gwmanatin Nijeriya ta gagauta daukar matakin kawo karshen wannan cin mutuncin da ake yi mana.

Share.

About Author

Leave A Reply