‘Yan Sanda A Jihar Bauchi Sun Kama Mutum 20 Da Laifin Aikata Fyade

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi ta tabbatar da kamun mutum 20 da ake zargi da aikata fyade  a fadin jihar, jami’in watsa labaran rundunar, Mr Ahmed Wakili, ya bayyan haka ranar Talata a tattaunawarsa da mabema labarai a garin Bauchi,

Ya ce, an kama mutanen ne a binciken da aka gudanar a kanannan hukumomi 20 da ke fadin jihar.

Wakili ya kuma ce a tsakanin watan Agusta zuwa Satumba ne aka samu wadanna rahoton.

Ya kuma ce yawancin wadanda aka kama sun amince da aikata laifinsu.

“Yawancin wadanda aka kama sun amince da aikata laifinsu kuma muna shirye shiryen zarcewa da su kotu don hukunta su,” inji shi.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai don ganin bayan dukkan masu aikata laiffuka, ta yadda za a hukunta su.

Ya kuma shawarci masu aiki da keken NAPEP su lura da fasinjojin da suke dauka don a kwai masu cutar da ‘yan keken NAPEP a ‘yan kwanakin nan.

Share.

About Author

Leave A Reply