‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Makanike A Gaban Kotu Bisa Zargin Satar Mashin A Kaduna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wani magidanci dan shekara 32, Sani Shehu, a ranar Talata ya bayyana a gaban Kotun Majistare da ke Kaduna, kan zargin satar babur da kudinsa ya kai N230,000.

 

‘Yan sanda sun tuhumi Shehu, wanda ke zaune a Kaduna da laifin sata.

 

Dan sanda mai gabatar da kara, Insp Chidi Leo, ya fadawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Janairu da misalin karfe 9 na dare. a Abakpa Road, cikin garin Kaduna.

 

Leo ya yi bayyana  cewa wanda ya kawo karar, mai suna Haruna Mairago, wanda ke zaune a Ungwan Sarki, Kaduna, ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Gabasawa da ke Kaduna.

 

Ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya saci babur din wanda Mairago ke ajiye a gaban shagon sayar da kayayyaki a kan titin Abakpa, Kaduna.

 

Laifin, in ji shi, ya ci karo da tanadin Sashe na 207 na Dokar Penal Code na Jihar Kaduna, 2017.

 

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

 

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi N100, 000 tare da mutum biyu da za su tsaya masa.

 

Share.

About Author

Leave A Reply