‘Yan Sanda Sun Kama Dalibai 16 Suna Daukar Rantsuwar Shiga Kungiyar Asiri A Neja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa, ta samu nasarar kama dalibai 16 ‘yan jami’ar Ibrahim Babangida Lapai a yayin da suke rantsuwar shiga wata kungiyar asiri a garin Lapai.

Jami’in watsa labarai na rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya sanar da haka a takardar sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Minna ranar Talata.

”A ranar 7 ga watan Yuli da tsakar dare bayan da aka samu bayanai na sirri, jami’anmu suka kai samame inda suka kama wadanda ake zargin  a yayin da suke shirin shiga kungiyar.

“An kama sune suna kokarin shiga wata kungiyar asiri mai suna Black Axe a unguwar Gwaranyo lodge, na garin na Lapai yayin da suke kokarin shiga kungiyar.

“Cikin kayayyakin da aka kama a hannun su sun hada da adduna, hular sojoji da kuma tukunyar taba wiwi,” inji shi.

Ya kuma ce za a gurfara dasu a gaban kotu da zaran an kammala bincike.

 

Share.

About Author

Leave A Reply