‘Yan Sanda Sun Kama Wani Matashi Bisa Zargin Barazanar Kisa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne ‘yan sanda a jihar Legas suka gurfanar da wani matashi mai suna Olamilekan Azeez a gaban kotun majastare da ke Badagry bisa laifin yin barazanar kashe wani mai suna Alhaji Kamaldeen Owoyemi.

Ana tuhumar matashin ne da laifin yi barazana ga rayuwar wani.

Dan sanda mai gabatar da kara, ASP. Clement Okuomose, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Disamba da misalin karfe 12.05 na rana a yankin  Oseni da ke Araromi a Legas.

Okuomose ya kara da cewa, wanda ake zargi ya yi barazanar kashe Alhaji Kamaldeen Owoyemi da adda.

Ya ce, laifin ya sabawa shashi na 56 na dokokin manyan laifukka na jihar Legas na shekarar 2015.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin yayin da aka karanto masa laifukan.

Daga na ne alkalin kotun, Lazaru Hotepo, ya bayar da shi beli akan N50,000, ya kuma daga kara zuwa ranar 26 ga watan Janairu don cigaba da sauraron shari’ar.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply