‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Fashi Da Makami 154 A Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke wasu ‘yan fashi da makami su 154 a sassan jihar Kano daban daban a cikin watanni 3 da suka wuce.

Jami’in watsa labarai na rudunar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da haka a sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Lahadi.

DSP Haruna ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a sassan jhar Kano daban daban a wani samame da aka gudanar a cikin watanni uku.

Ya kuma ce, an kama ‘yan fash da makami 14, ya daba 143 da masu garkuwa da mutane da dama da kuma masu laifukka daban daban.

Jami’in watsa labaran rundunar ya kuma ce, rundunar ta kama bindiga kirra AK-49 guda 1 da AK-47guda 2 da kuma wasu muggan makamai da kuma kwayayoyin sa maye da sauran kayan da aka haramta mu’amala da su.

Ya kuma kara da cewa, a ranar 20 ga watan Maris  ‘yan sanda sun samu nasarar kama wani mai suna Musa Abubakar, 23, wadanda suka hada baki suka kai wa wani mai suna Hassan Shariff hari a kauyen Gunduwawa da ke kan hanyar Kano zuwa Hadejia.

Ya kuma ce, za a gabatar da dukkan wadanda aka kama zuwa kotu a hukunta su yadda doka ta tanada, da zaran an kammala bincike.

Share.

About Author

Leave A Reply