‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kisan ‘Yan Bindiga 10 A Sakkwato

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da labarin kisan ‘yan ta’adda 10 a wani hari da jami’an tsrao suka kai kauyen Tara da ke karamar hukumar Sabon Birni ranar Juma’a da safe.

Jami’in watsa labarai na rundunar, ASP Sunusi Abubakar, ya sanar da haka a tattaunawarsa da manema labarai a garin Sakkwato, ya kuma ce, wasu mutum 3 na karbar magani a asibitn kashi na garin Wamakko sakamakon raunukan da suka samu a harin.

Ya kuma kara cewa, tuni kwamishinan ‘yan sanda jihar Mr Kamaldeen Okunlola, ya ziyarci a’lummar yankin inda ya tabbatar musu da cikkaken tsaro a yankin.

“Rundunar ta tura dakaru na musamman don kara tsaurara tsrao a yankin tare da kuma tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da hannu a aika-aikar.

“Muna kuma kira ga al’umma jihar Sakkwato da su cigaba da ba jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ya kamata don maganin ‘yan ta’adda a fadin jihar,” inji shi.

Ya kuma shawarci al’umma jihar su lura da masu zirga zirga a yankunan don kai rahotn duk wani da basu gane taken takensa ba ga juami’an tsaro don a dauki matakin da ya kamata.

 

Share.

About Author

Leave A Reply