‘Yan Ta’adda Sun Sace Xalibai Da Malamai A Makarantar Mata A Jihar Kebbi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotanni sun bayyyana cewar, yan bindiga sun sace xalibai da malamai a makarantar mata da ke  Birnin Yauri, Jihar Kebbi.

Babu cikakakken bayani kan yanda harin ya afku zuwa yanzu, sai dai wasu rahotanni na cewa cikin waxanda aka rutsa da su har da jamiín tsaro xaya. Babu tabbacin cewa ya mutu duk da rahotannin da ke nuni da haka.

Ýan bindigar, wanda su ke kan mashuna, an ce sun fito ne daga dajin Rijau, inda su ka afka zuwa makarantar bayan da su ka ci qarfin ýan sandan da ke gadin makarantar, kamar yadda bayanai su ka nuna.

Aqalla xalibai 30 aka sace tare da malamai 3, bayan da ýan bindigar su ka samu nasarar shiga makarantar yayin da wasu ke xauki ba daxi da jamián tsaro a qofar makarantar, kamar yadda wani jamiín tsaro ya shaida mana.

Wani shaidun gani da ido da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce harin ya afku ne da misalin 12:30 na rana. Daga cikin waxanda aka xauke har da mataimakin shugaban makaranta da kuma malama xaya, in ji shi.

Wannan dai shi ne karo na uku da ýan bindiga su ka yi garkuwa da xalibai a makarantu.  30 ga Mayu, ýan bindiga sun sace xalibai islamiya a Tegina, Jihar Naija. Sai kuma bayan mako biyu, makarantar Nuhu Bamali foli da ke Zariya, Jihar Kaduna inda su ka sace xalibai da malamai a nan ma.

Share.

About Author

Leave A Reply