Yaqi Da Rashawa A Mulkin Dimokiradiyya Nada Matukar Wahala – Shugaba Buhari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, yaqi da cin hanci da rashawa a tsarin dimokiraxiyya aiki ne mai wahalar gaske a cimma.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Arise wanda aka watsa a ranar Alhamis.

A cewarsa, yaqi da cin hanci da rashawa ba shi da sauqi a gare shi tun lokacin da ya zama zavavven Shugaba na dimokiraxiyya shekaru shida da suka gabata.

Amma, ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi nasarar sassauta jami’an gwamnati ba tare da hayaniya ba.

Buhari ya tuna cewa, an samu nasarori da yawa a yaqi da cin hanci da rashawa lokacin da yake Shugaban qasa na mulkin soja a farkon shekarun 1980 lokacin da aka tura mutane da yawa zuwa gidajen yari kafin an tunkuxe shi.

A lokacin da yake bayyana irin yadda ake tafiyar da mulkin qananan hukumomi Shugaban ya yamutsa fuska kan yadda tsarin qananan hukumomi ke gudana, yana mai cewa, gudanar da mulkin qananan hukumomin kusan babu shi a qasar.

Ya kawo misali da yanayin da gwamnonin jihohi suka ci gaba da kashe wa qananan hukumomin kuxi, yana mai cewa, a yanayin da aka ware Naira miliyan 300 ga qananan hukumomi kuma aka ba su Naira miliyan 100 ba adalci ba ne.

A kan ayyukan ‘yan bindiga da masu satar mutane musamman a shiyyar Arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, Shugaba Buhari ya ce, ya bai wa ‘yan sanda da sojoji umarnin cewa su zama marasa tausayi akan ‘yan bindiga da masu satar mutane da ke ta’addanci a faxin qasar.

Ya ce, ya gaya wa jami’an tsaro su yi amfani da yaren da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ke fahimta.

“Matsala a arewa maso yamma, kuna da mutane a can suna satar shanun juna suna qone quuyukan juna. Kamar yadda na ce, za mu yi amfani da su a yaren da suke fahimta. Mun bai wa ‘yan sanda da sojoji qarfi su zama marasa tausayi. Domin a cikin ‘yan makonni kaxan za a sami bambanci,” in ji Buhari.

Ya ce, “Saboda mun faxa masu idan muka nisanta mutane daga gonarsu, za mu shiga cikin yunwa, kuma gwamnati ba za ta iya sarrafa jama’a ba. Idan ka ba da damar yunwa, gwamnati za ta kasance cikin matsala kuma ba ma son zama cikin matsala.”

“Mun riga mun gano bakin zaran matsalar, don haka muna ba da daxewa ba za ku ga bambanci,” in ji shi.

Dangane da rikicin manoma da makiyaya, shugaban ya ce, matsalar ta ci gaba saboda tsofaffin hanyoyin shanu da wuraren kiwo an keta su ta hanyar ci gaba, ya qara da cewa, waxanda suka karvi irin waxannan tsare-tsaren gargajiyar za a fatattake su.

Dangane da batun yaqi da ta’addanci, Buhari ya yi watsi da ikirarin cewa akasarin mambobin qungiyar ta Boko Haram ‘yan qasashen waje ne.

A cewarsa, yawancin ‘yan qungiyar ta Boko Haram ‘yan Nijeriya ne, yana mai cewa hakan ya qara tabbata ne ta hanyar Gwamna Babagana Zulum na Borno.

Shugaban ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yi matuqar aiki don yaqar ‘yan ta’adda da masu tayar da qayar baya amma matsalar da ke cikin Arewa maso gabas tana da matuqar wahalar sha’ani.

 

Share.

About Author

Leave A Reply