Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Jan Hankali Ga Matasanmu Na Katsina

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Abdulganiyu Gambo

Yana da kyau matasanmu su kula sosai a wannan lokacin zaɓe da za a gabatar na ƙananan hukumomin Katsina, duba da yadda matasa suka fito neman takara a ko wanne fanni abu ne mai kyau.

Kuma abin murna ne duba da yadda aka bar matasanmu a baya a cikin harkokin siyasa.

Jan hankalina ga matasan da suka fito a ko wanne ɓangare na takara na ƙananan hukumomi, yana da ƙyau ku wayar da kan al’umma manufofinku idan kun kai ga karagar mulki wannan zai kara ba al’umma ƙarin ƙarfin gwiwa a zaɓe mai zuwa.

Saboda in kun duba baya marigayi tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’adua lokacin leman zaɓen Shugabancin ƙasa ya yi bayanin kudurorin shi guda bakwai wato ‘7 Point Agenda’ haka kuma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari shi ma ya zo da kudurori kala-kala waɗanda suka gamsar da al’umma suka zaɓe a lokacin neman zaɓensa har da na samarwa matasa aiki dubu dari biyar 500,000 wato (Npower) kuma Alhamdulillah.

Share.

About Author

Leave A Reply