Zaben Cike Gurbi: An Sace Ma’aikatan INEC Biyu A Zamfara

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Hussaini Baba, Gusau

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa an sace wasu ma’aikatan wucin-gadi biyu na Hukumar INEC.

Su dai wadannan Ma’aikatan na INEC an sace su ne a jiya Asabar bayan kammala zaben Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karamar Hukumar Bakura.

Baturen Zaben Cike gurbin, Farfesa Ibrahim Magawata ne ya bayyana batun Sace wadannan ma’aikata a yau Lahadi.

Farfesan ya kuma ayyana zaben a Matsayin wanda bai kammala ba sakamakon wasu matsaloli da aka samu.

  1. Kafin ayyana zaben a Matsayin wanda bai kammala ba dai, dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Tudu ne  kan gaba da yawan kuri’u 18,645, yayin da dan takarar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji ke da kuri’u 16,464.
Share.

About Author

Leave A Reply