Zaben Edo: Jam’iyyun Siyasa Sun Sa Hannu A Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne jam’iyyun siyasan da ke shirin fafatawa a zaben kujerar Gwamna da za a gudanar a jihar zabe suka sanya hannu a yarjejeniyar mutunta dukkan dokokin da ke tattare da zaben tare da kuma kaucewa tayar da hankali a yayin gudanar da zaben.

Janar Abdulsalam Abubakar (rtd.), shugaban tabbatar da zaman lafiya na kasa ‘National Peace Committee (NPC)’ kuma tsohon shugaban kasa, ya sanar da haka a taron da aka gudanar a garin Edo, yana mai cewa lallai yakamata a tabbatar da zaman lafiya a jihar Eddo.

Ya ce, “Kuna sane da cewa, tun daga shekarar 1999, ana samun tashin hankula a dukkan zabukkan da aka gudanar, wadanda tashe tashen hankulan suka kai ga kafa wannan kwamitin don tabbatar da dukkan zabukkan da za a gudanar a kasar nan an yi su cikin kwanciyar hankali ba tare da rikici ba.

“Muna bukatar da samar da Nijeriyan da za a cigaba da zaman lafiya duk da zaben da za a gudanar a kasar nan.’’

A jawabinsa, dan takara Gwamna a jam’iyyar PDP kuma Gwamna mai ci yanzu, Godwin Obaseki, ya ce shi da jam’iyyarsa za su tabbatar an gudanar da sahihin zabe ba tare da matsala ba, akan haka kuma ya sanya hannun akan yarjejeniyar zaman lafiyar.

“Bayan kasancewa na dan takara kuma ni ne babban jami’in tsaro na jihar, akan haka na fi kowa son zaman lafiya a jihar,” inji Obaseki.

Gwamnan ya kuma bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a kan zaben da su bayar da gudumawar ganin an yi zaben cikin kwanciyar hankali.

A nasa bangaren, dan takarar jami’iyyar APC, Osagie Ize-iyamu, ya yi alkawarin tattaunawa da masu goyon ganin an gudanar da zabe a cikin kwanciyar hankali.

“Muna godiya ga ‘yan kwamitin samar da zaman lafiya da kuma hukumar zabe INEC, haka kuma muna godiya ga Oba na  Benin a kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a jihar,” inji shi.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply