Zaben Edo: Mai Mala Buni Da Yahaya Bello Sun Gana Da Ize-Iyamu A Abuja

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamna Mai Mala Buni, Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC, ya gana da dan takarar jam’iyyar a zaben da aka yi a jihar Edo ranar Asabar din da ta gabata.

Buni, wanda kuma shi ne gwamnan Yobe ya tattauna da Ize-Iyamu, tare da Gwamna Yahaya Bello na Kogi a gidansa na Abuja ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne fitar dan takarar APC tun bayan zaben Gwamnan da aka yi ranar 19 ga Satumba a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa shugabannin jam’iyyar na kokarin bai wa dan takarar hakuri ne, don ya amince da sakamakon, wato na nasarar Gwamna Godwin Obaseki na PDP a kansa.

Wata majiyar da ta nemi a boye sunanta, ta ce zaman ya karkata ne kan yadda Ize-Iyamu zai amince da sakamakon zaben na Edo.

Jagorancin APC cikin wani sanarwar da suka fitar bayan zaben, sun taya Obaseki, mataimakinsa da kuma PDP murnar lashe zaben.

APC a cikin sanarwar da ta yi mai dauke da sa hannun Gwamna Buni ta yi nuni da cewa sakamakon zaben nasara ne ga dimokuradiyya.

“Zaben Gwamnan da aka yi ranar 19 ga watan Satumba, 2020, ya kare. Kuma INEC ta ayyana Godwin Obaseki na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

“Muna taya shi murnar nasarar da ya yi, da kuma dukkan al’ummar jihar Edo da sauran ‘yan Nijeriya.

“Da lumana da sakamakon zaben ya nuna nasara ne ga dimokuradiyya,” inji APC.

Jam’iyyar tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun taya Obaseki murnar lashe zaben.

A cewarta, hakan ne zai karfafa turbar dimokuradiyya.

Jam’iyyar ta kuma yaba wa tsohon Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da sauran mambobin jam’iyyar kan goyon bayan dan takararta da ta yi.

 

Share.

About Author

Leave A Reply