Zaben Kananan Hukumomi: Gwaman Legas Ya Bukaci Jama’a Su Fito Su Kada Kuri’arsu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Legas, Mr Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira na musamman ga al’ummar jihar dasu fito kwansu da kwarkwatar su don kada kuri’asu a zaben kananan hukumin da ake gudanarwa a yau Asabar.

Gwamna Sanwo-Olu ya yi wannan kiran ne bayan da ya kada kuri’arsa a mazabarsa ta 019,Femi Okunnu/Lateef Jakande Avenue da ke karamar hukumar Eti-Osa.

Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya ya sanar da cewa, Gwamnan da matarsa, Ibijoke, sun isa rumfar zaben ne da misalin karfe 11.03 na safe sun kuma kada kuri’ar sune da misalin karfe 11.08 daidai.

Ya kuma nuna jin dadindsa a kan yadda ake gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba, ya kuma yi kira ga al’umma su tabbatar da sun sauke nauyin su na jefa kuri’a don a tafi dasu a harkar domokradiyya.

 

Share.

About Author

Leave A Reply