Zaben Ondo: INEC Ta Nemi Jam’iyyu Su Yi Gaskiya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su samar da yanayin da za a yi zaben gaskiya da kuma adalci a jihar Ondo.

 

Rahotanni na nuna cewa ranar 10 ga watan Oktoba za a a yi zaben Gwamna a jihar.

 

Antonia Okoosi-Simbine, Kwamishiniyar kwamitin sa ido kan zabe da jam’iyyu ta INEC, ce ta bada shawara a Akure ranar Jumma’a.

 

Ta bayyana hakan ne yayin wani zaman masahala da aka shirya wa jam’iyyun da aka yi wa rajistar shiga zaben gwamnan.

 

Okoosi-Simbine ta yi bayanin cewa jam’iyyun siyasa na taka gagarumar ruwa wajen ganin mambobinta sun yi abin da ya dace don yin zabe cikin lumana da kuma adalci.

 

A cewarta, jam’iyyun su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, wanda zai haifar da kariya ga rayuka da kuma dukiyar jama’a.

 

Kafin nan, Hamza Fassi-Fihri, Mai gudanar da Cibiyar tallafin zabe na Turai, Hamza Fassi-Fihri ya ce jam’iyyun siyasa su ne a matakin farko wajen wanzar da zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakanin jam’iyyu.

 

Fassi-Fihri, wanda ya yi bayanin cewa gasar da ake ne a siyasa ke jawo rikice-rikice, ya ce masalaha zai iya kau da batun zuwa kotu ka kara.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply