Zamfara 2023: Dauda Lawal Ya Zaɓo Gogaggen Ɗan Siyasa A Matsayin Mataimaki

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ɗan takarar gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal ya sanar da wanda zai yi mishi mataimakin gwamna a zaɓen 2023.

Dauda Lawal ya bayyana Malan Mani Malan Mummuni a matsayin abokin takararshi ne jiya Litinin a gidansa dake Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Masu fashin baƙin siyasa sun bayyana Malan Mani a matsayin gogaggen ɗan siyasa da ke da nauyi a siyasar Jihar Zamfara. Ya fito ne daga ƙaramar hukumar Bukkuyum.
Tsohon Daraktan na First Bank kuma Shugaban Kamfanin Credent Capital ya yi amfani da ziyarar da masu ruwa da tsakin jam’iyyar PDP suka kai mishi wurin gabatar musu da mataimakin nasa, kamar yadda ya bayyana a ingantattun shafukansa na sada zumunta.
Ya ce: “Jiya a gidana dake Gusau, cikin farin ciki na amshi baƙuncin shugabannin jam’iyyar PDP na ƙananan hukumomi 14, mutum biyar masu riƙe da muƙaman jam’iyya daga kowacce ƙaramar hukuma, da ‘yan takarar sanata uku da muke da su.

“Dukkansu sun zo ne domin gaisuwar sallah da kuma tattauna muhimman hanyoyin da za mu bi don nasarar jam’iyyarmu a zaɓen 2023.

“Bayan muhimmiyar tattaunawa mai cike da ma’ana, na yi amfani da wannan dama wurin sanar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyarmu wanda na zaɓa a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna – Malan Mani Malan Mummuni (Masamar Mudi). Wanda ya kasance gogaggen ɗan siyasa.” Inji shi.

Share.

About Author

Leave A Reply